27 Nuwamba 2019 - 05:05
 Ana Gudanar Gasar Kur'ani Ta Share Fage A Ingila

Kamfanin dillancin labaran iqna, mahardata kur’ani daga cikin muuslmin kasar Birtaniya sun siga gasar share fage ta gasa mai zuwa.

(ABNA24.com) Bangaren kasa da kasa, ana gudanar da gasar share fage ta kur'ani mai tsarki a birnin Landa wasu biranen Ingila.

Kamfanin dillancin labaran iqna, mahardata kur’ani daga cikin muuslmin kasar Birtaniya sun siga gasar share fage ta gasa mai zuwa.

A ranakun 14 da 15 ne dai za a kai ga mataki na karshe na wannan gasar kur’ani mai tsarki ta share fage a kasar ta Birtniya.

Bnagarorin da za a gudanar da gasar a cikinsu sun hada da bangare na juzui 5 da kuma juzui 15 da kuma juzui 30.

Wadanda suka zo na daya da na biyu da na uku a dukkanin bangarorin za su samu kyautuka da za su hada har da kudade.

Baya ga haka kuma daga cikinsu ne za a zabi wadanda za su wakilci kasar a gasar kr’ani ta kasa da kasa da ake sa ran gudanarwa a kasar ta Birtaniya.

Haka nan kuma baya ga kyautar kudade za a basu tikitin tafiya Haji da Umra kyauta domin sauke farali.



/129